Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, a wannan zamani da al’ummar yau suka fi kowane lokaci buƙatar dawo da kyawawan misalai na asali waɗanda ke gina hali na ainihi, sake duba fannoni daban-daban na “salon rayuwar Fatimiyya” abu ne da baya buƙatar inkari.
Sake duba tarihin Musulunci yana nuna cewa rayuwar Sayyida Fatima Zahra (AS), ba kawai abin koyi na tarihi ba ce, a’a, taswira ce cikakkiya ga rayuwar ɗan Adam da imaninsa a kowane zamani. Kamfanin Dillancin Labaran Hauza zai gabatar wa masu karatu wasu fannoni daban-daban na wannan abin koyi marar misaltuwa na tarihi a sassa daban-daban.
Sanin Imami a cikin tsananin wahala da bakin ciki; lokacin da “Rayuwar Imam” ta fi muhimmanci fiye da kowanne irin ciwo na kashin kai
Sayyida Fatima (SA) ta buɗe idanunta cikin wahala. Ciwo ya mamaye dukkan jikinta, gidan kuwa har yanzu cike yake da hayaƙi, Fidda idanunta cike da hawaye, tana tare da ita. Kafin Sayyida (AS) ta tambayi halin da Hasan da Husaini suke ciki, kafin kuma ta yi makoki saboda Muhsin ɗinta; sunan Imaminta ta fara kira.
Ta tambayi halin da Imam Ali (Mazlumi) ke ciki, lokacin da ta sami labarin cewa an tafi da shi zuwa masallaci, da jin haka ta manta da dukkan ciwo da wahalhalun da take ciki, ta nufi masallaci nan take. Barazanar da Sayyida Fatima (AS) ta yi a cikin masallaci ce ta ceci ran Imam Ali (AS), Ran Imamin zamaninta.
Madogara:
Biharul-Anwar, juzu’i na 43, shafi na 47.
Sanin Imami a Cikin Tsananin Wahala da Baƙin Ciki; Lokacin da “Ran Imam” Ya fi Muhimmanci Fiye da Kowane Irin Ciwo na Ƙashin Kai
Hauza/ Sake duba sahun farko a tarihin rayuwar Fatimiyya yana nuna kasancewar Siddiƙa Al-kubra (AS) a cikin tsananin musiba, wahala da zafi mai ratsa zuciya, kafin kallon kowace irin damuwa ta kanta, ta fara tambayar halin Imamin zamaninta; abin koyi marar misaltuwa gareta, wanda ya nuna cewa kare wilaya shi ne jan layi da kuma falsafar rayuwa a al’adar Fatimiyya.
Ra'ayinka